Fasinjoji 18 sun kone kurmus a wani hatsari da afku a jihar Neja


Fasinjoji goma sha takwas a wata motar bus mai daukar mutane 18 sun kone kurmus a wani hatsarin sassafe da ya wakana a Gidan Kwano hanyar Minna-Bida a karamar hukumar Bosso da ke jihar Neja.

An tattaro cewa motar ta fito ne daga jihar Lagas zuwa wani wuri da ba a sani ba amma dai hukumomi sun ce ta yiwu tana a hanyarta ta zuwa Kano ko jihar Sokoto.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa hatsarin wanda ya afku da misalin karfe 3:00 na tsakar daren Lahadi, ya wakana ne bayan motar ta yi karo da wata babbar motar daukar kaya da aka faka a hanyar kafin ta kama da wuta.

Kasancewar abun ya faru a lokacin da mutane ke bacci, an tattaro cewa ba a samu kai agaji ba har sai zuwa 5:00am lokacin da mutane suka fara taruwa.

Zuwa lokacin, fasinjojin sun babbake kurmus har ba a iya gane su.

The Nation ta kuma tattaro cewa an ceto biyu daga cikin mutanen sannan aka kwashe su zuwa asibtin IBB inda daya daga cikinsu ya rasu yayin da dayan ke cikin mummunan yanayi.

Jaridar Punch ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar Neja, DSP Abiodun Wasiu, ya tabbatar da lamarin cewa an binne mutanen a kusa da inda hatsarin ya afku.

Ya kuma ce lambar motar ma ta kone fiye da tunani.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN