Mota ta yi hatsari da Deliget na APC bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa wasu sun mutu (Hotuna)


Wakilai biyu daga jihar Rivers da suka halarci zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da aka kammala a Abuja sun mutu a wani hatsarin mota. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

An bayyana sunayen mutanen da Onimiteim Vincent da Barista Prince Loveday Motats. 

An tattaro cewa Motar Toyota Sienna da suke ciki kan hanyarsu ta zuwa birnin Fatakwal ta yi hatsari ta yi kaca-kaca yayin da direban ke kokarin kaucewa yin karo taho-mu-gama da wata motar. 

An ce Onimiteim ya mutu nan take yayin da wasu mutum biyar kuma aka kai su asibiti inda daga bisani Motats ya rasu.

Wani da ke cikin motar, Innocent Amadi, ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Laraba, 8 ga watan Yuni, kusa da gidajen malmaan Jami’ar Abuja (UniAbuja).


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN