Limamin Cocin Katolika ya kori manbobin Cocin da basu da katin zabe PVC ya hana su shiga Coci


Wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna wani limamin cocin Katolika yana rokon mambobin da ba su da katin zabe na dindindin (PVC) su koma gida

Mutane da yawa sun raba bidiyon akan dandalin micro-blogging, Twitter, da kuma akan YouTube. 

Limamin Cocinnya ce:

"Babu wata fa’ida a ce Kiristoci sun cika cocin, amma a lokacin zabe, kadan ne daga cikinsu suka fito domin kada kuri’a". 

“Don haka, yana nufin adadin mu, yawan mu ba komai bane. Muna son Kiristoci su ɗauki alhakinsu da aikinsu da muhimmanci.” 

Sai firist ɗin ya umurci waɗanda ke da PVC ɗin su su shigo cocin kuma waɗanda ba su da su koma gida. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN