Yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji 50 a hanyar Sokoto zuwa Gusau


Kimanin mutane 50 ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su bayan wani hari da suka kai kan wasu motoci a kan hanyar Sokoto zuwa Gusau.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wadanda aka kama suna dawowa ne daga wani daurin aure a garin Tambuwal na jihar Sokoto a yammacin ranar Asabar, inda ‘yan bindigar suka far wa motocinsu. An kai harin ne wata motar bas da wata motar da ke jigilar bakin daurin auren da kuma wasu motoci masu zaman kansu guda biyu. 

Daya daga cikin fasinjojin, Lawal Ja'o ya shaidawa jaridar cewa an kai harin ne a kusa da Dogon Awo, a karamar hukumar Tureta.

Yace; 

"Mun fara jin karar harbe-harbe kafin a fara kai wa motar farko hari", inda ya kara da cewa sama da mutane 50 ne aka yi awon gaba da su.

“Mun ci gaba da jin muryoyi da kururuwar abokan aikinmu da abokanmu amma babu abin da za mu iya yi. Bayan mun ji shigowar jami’an tsaro sai muka fito daga cikin daji muka gano kanmu.” 

Wani fasinja Jabiru Shehu wanda ya yi ikirarin cewa an sace fasinjoji kusan 50 ya ce; 

“Mun hadu da motoci hudu babu kowa dauke da wasu kayayyaki da suka hada da waya da wasu jakunkuna na tafiya. Muna nan sai wasu ‘yan sanda daga Tureta suka iso wurin.

"Daga abin da na ji, sun kasance fiye da mutane 50 tare da 'yan fashin saboda muna can kuma wasu matafiya da suka gudu cikin daji suka dawo babban titin."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN