Kotu ta yanke wa yar aikin gida hukuncin kisa bayan ta kashe mahaifiyar tsohon Gwamna


Mai shari’a Efe Ikponmwonba na kotun manyan laifuka 1 da ke birnin Benin a jihar Edo, ya yanke wa Dominion Okoro, ‘yar aikin gidan marigayiya Madam Maria Igbinedion, mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Edo, Lucky Igbinedion, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe tsohuwar mai shekaru 85 da haihuwa a gidanta da ke GRA Benin City a ranar Disamba 2 2021, kafin ta gudu da kayan adon ta.

Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo cewa Okoro wanda ta yi hidimar gidan marigayiyar tsawon shekaru, ta kashe ta ne saboda tana so ta kwashe kudinta da kayanta. Lokacin da aka kama ta, Okoro ta ce marigayiyar bata taba bata mata rai ba. 

''Na kashe Mama (Madam Maria Igbinedion) domin daukar kudinta. Ba ta bata min rai ba. Tana kwance akan gadonta, da misalin karfe 12:01 na safe ranar 2 ga Disamba, 2021, na yi amfani da tabarya na buga mata kai, tana ihu tana neman taimako, amma Mai gadi bai ji ihun Mama ba daga baya ta rasu.

Na jira har karfe 4 na safe ranar 2 ga Disamba, 2021, kafin na bar gidan da N100,000 na Mama, agogon hannu, da kayan adon. Na tsere zuwa jihar Cross River, amma daga baya ‘yan sanda suka kama ni.”

Bayan furucinta na ikirari, an kama Dominion da 'yar uwarta. An gurfanar da ‘yar uwarta Patience Okoro a gaban kotu.

Da yake yanke hukunci a shari’ar a ranar Litinin, 20 ga watan Yuni, Mai shari’a Ipkonwonba ta samu Dominion da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume uku da aka shigar mata. Kotu ta yankewa Dominion hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kisa da kuma fashi da makami yayin da ta kama ta daurin rai da rai bisa aikata laifuka biyu da suka shafi shafa abubuwa masu cutarwa ga marigayiya Madam Igbinedion. 

'Yar'uwar mai laifin da aka tuhume ta da laifin kisa Kotu ta sallame ta kuma ta wanke ta. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN