Jarabawar NCEE: Dalibai 15 sun ci maki 1 kacal , yar Sokoto ta fi kowa cin maki


A kalla dalibai 15 ne suka ci maki 01 kacal a yayin da hukumar shirya jarrabawa da Najeriya, NECO, ta fitar da sakamakon jarrabawar shiga karamar ajin sakandare
.

The Punch ta rahoto cewa jarrabawar ta NCEE da NECO ta yi na shiga ajin farko ne a kananan ajijuwan sakandare a makarantun sakandare na tarayya.

Jarrabawar ta 2022 an yi ta ne a ranar 7 ga watan Mayun 2022 a Nigeria da Jamhuriyar Benin da Togo.

Yayin bada kididdigan a Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya a ranar Litinin, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya ce:

"Jihar Anambra ta zo ta uku da dalibai 5,335; cikin 5,070 sun rubuta jarrabawar yayin da 265 ba su rubuta ba. Jihar Zamfara ce ta hudu da dalibai 4,500, cikinsu 3,745 sun rubuta jarrabawar yayin da 755 ba su rubuta ba.

"Dalibar da ta fi kowa samun maki mai yawa ita ce Ajidagba Akanke, yar asalin Jihar Sokoto mai lamba 542121DG. Cibiyar da ta rubuta jarabawar ita ce Makarantar Karamar Sakandare ta Oshodi, Tolu Complex, Apapa Legas, ta kuma ci maki 201. Obot Idara, yar asalin Jihar Akwa Ibom mai lamba 550470BF ta zo na biyu da maki 200. Ta rubuta jarrabawar a Kwallejin Jiha ta Ete, Ikot Ekpene.

"Mafi mafi karanci shine 01, kuma wasu dalibai 15 daga jihohi daban-daban suka samu maki daya kacal din. Jihar da ta fi karancin daliabai da suka yi rajista ita ce Jihar Kebbi, da dalibai 74."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN