Harin Jirgin kasa: Jagoran sasanci da 'Yan bindiga ya janye, ya aike sako ga FG, duba ka gani


Ragowar fasinjoji 50 da aka sace a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna suna fuskantar barazanar cizon macizai da ciwuka masu matukar illa ga rayukansu.

Mallam Tukur Mamu, wanda shi ne ke jagorantar sasancin tsakanin gwamnatin tarayya da 'yan bindigan ya bayyana hakan a ranar Litinin.

Rahoton Punch ya bayyana cewa 'yan bindigan sun sako mutum 11 daga cikin 61 dake hannunsu bayan kwashe kusan watanni uku a hannun 'yan ta'addan.

Mamu ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kokari wurin ceto sauran fasinjoji 50 da ke hannun 'yan ta'addan kafin lokaci ya kure.

Hakazalika, ya sanar da janyewa daga cikin masu sasancn. Babu dalilin da ya bayar da ya wuce na kan shi.

Kamar yadda yace, halin da sauran fasinjoji ke ciki na kara tabarbarewa sakamakon zama da suke cikin hali mai hatsarin gaske.

Ya ja kunne cewa ta yuwu wasu ba za su fito da ransu ba idan har ba a dauka matakin gaggawa ba wurin tabbatar da an ceto su daga sansanin masu garkuwa da mutanen.

"Wannan ba lokacin siyasantar da lamurra bane. Rayukansu suna da amfani, 'yan Najeriyan da basu da laifin komai suna hannunsu. Kullum lafiyarsa kara tababarewa take yi. Ko dabbobi ne babu kula, da kyar su iya jure wannan muhallin da aka tsare su na kusan watanni uku.

“Na san cewa gwamnati ta sani kuma ta ji abinda fasinjojin da aka sako suke fadi. Abun na bani takaici idan lamurra irin haka aka bar su ba tare da an gaggauta shawo kansu ba.

Mmu wanda shi ne mawallafin jaridar Desert Herald, ya ce baya da rashin kulawar likitoci tare da abinci mara kyau, rashin tsaftar muhalli, fasinjojin na fama da rayuwar daji wanda hakan yasa wasu suka kamu da ciwuka har suna aman jini.

Ya kara da cewa, "Zan iya tabbatar muku da cewa akwai macizai a dajin. Wasu daga cikinsu duk macizan sun sare su saboda sau da yawa suna bayyana cikin dare. Magungunan gagajiya ake basu su sha.

"Saran kamar yadda muka sani za su iya kasancewa barazana ga rayuka. Gwamnati ce kadai hukumar da ke da damar kawo karshen wannan lamarin da gaggawa idan ta so. Idan kuma an bi lamarin yadda ya dace, cikin kwanaki ko makonni za a sako su. Mun ga misali da yadda aka sako mutum 11.

“Ina yawan fadi, a irin wannan hali da ya jibanci rayukan 'yan kasa, gwamnati dole ta shirya hakuri da wasu tsarikanta kuma ta dauka hukunci marasa dadi.

“Idan za mu iya jure 'yan siyasa masu satar biliyoyi kowacce rana wanda sakamakon hakan talauci da rashin tsaro ke cigaba, a gani na za a iya amfani da wasu kudin a karbo mutane idan bukatar hakan ta taso."

Legit.ng ta tuntubi daya daga cikin iyalan fasinjojin domin jin ta bakinta, ta bayyana cewa ba su riga sun ji bayanin janyewa daga sasancin ba da Malam Tukur Mamu ya yi.

Ta sanar da cewa, tabbas labaran da suka ji daga bakin wadanda aka sako mummunan labari ne wanda ya sake daga musu hankali.

"A taya mu da addu'a, wannan babbar jarabawa ce ta same mu. Tun bayan sace su da aka yi, ba mu sake samun kwanciyar hankali ba. Bacci kanshi ba cikakke muke yi. A taya mu da addu'a," tace.

Fasinjojin da aka yi garkuwa da su sun kwashe kwanaki sama da 70 a hannun miyagun kafin su sako su bayan tsananin sasanci da aka yi da su.

Daily Trust ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan sun sako fasinjojin shida mata da maza biyar a ranar Asabar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN