Kotu ta bada umarnin kwace kadarorin dan Dasuki na wucin gadi N90m


Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kwace wani kadara na wucin gadi na Naira miliyan 90 da ake alakantawa da Abubakar Atiku Dasuki, dan tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mohammed Sambo Dasuki.

Mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin mayar da kudaden ne a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni, yayin da yake yanke hukunci a kan wata bukatar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta shigar.

Mai shari’a Nwite ta kuma umurci hukumar EFCC da ta buga wannan umarni na kwace kadarorin na wucin gadi a shafinta na intanet domin masu sha’awar su nuna dalilin da ya sa ba za a ba wa gwamnatin tarayya kadarorin na dindindin ba.

Daga nan sai alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 14 ga watan Yuli.

Lauyan EFCC, Olanrewaju Adeola ya ce ana zargin cewa an samu kadarorin ne da wasu kudaden ta hanyar haram.

Adeola ya bayyana wannan kadara a matsayin wani gida mai dakuna bakwai da aka kebe tare da bene da kuma dakunan masu hidima guda biyu da aka bayyana sunayensu da House No. D1064, Brains and Hammers Estate, Apo, Abuja.

A cikin takardun kotu, EFCC ta yi ikirarin cewa mai wannan kadara ya amince ya mikawa gwamnatin tarayya.

A cikin wata takardar rantsuwa, ta bayyana cewa, 

“A cikin binciken da ake yi, an gayyaci Abubakor Atiku Dansuki zuwa hukumar inda bisa radin kansa ya bayar da sanarwar cewa bai aiwatar da wata kwangila da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ba. don haka babu wani kudi daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) da suka hada da N90,000,000 00 da ONSA ta biya wa Brains da Harnmars Ltd asusun Fidelity Bank mai lamba 4010167275 da ONSA ta siyan dakuna bakwai da aka ware. Duplex with basement and 2 Servant Rooms, at House No 01064 at the Brains and Hammers Estate, Apo.Abuja da sunan Abubakar Atiku Dasuki.

“Abubakar Atiku Dasuki, a cikin sanarwarsa, bisa radin kansa ya amince da mika kadarorin ga gwamnatin tarayyar Najeriya ta hannun hukumar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN