Wata Kotun Majistare da ke Iyaganku da ke Ibadan, a ranar Laraba, ta yanke wa wani matashi dan shekara 23, Isaac Dumabara, hukuncin daurin wata daya a gidan yari, bisa samunsa da laifin satar tukunyar miya da nama na Naira 40,000 a gidan abinci. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
NAN ta ruwaito cewa Majistare S. A Adesina, wanda ya samu Dumabara da laifin sata, ya yanke masa hukunci ba tare da zabin biyan tara ba.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, ASP Sikiru Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa Damubara ya kuma saci injinan gas guda uku, stabilizer da kuma takalmin Adidas guda biyu daga gidan cin abinci na Pleasure Summit da ke titin Magara a Iyaganku, a birnin Ibadan.
Ibrahim ya kuma shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya kuma saci wani talabijin mai inci 42 wanda kudinsa ya kai N200,000.
Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 390(9) na dokokin manyan laifuka na jihar Oyo, 2000.