Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da kisan wani tsohon dan majalisar jihar, Hon. Nelson Emeka Achukwu , da wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ba suka aikata. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya tattaro.
An yi garkuwa da Okoye tare da mataimakinsa da misalin karfe 10:15 na dare a gidansa a ranar 9 ga watan Yuni kuma an tsinci gawarsa an yanke kansa a tsakanin iyakar Uke da Ukpor a yammacin ranar Talata, 22 ga watan Yuni.
Majiyoyin iyalan sun ce abin ya wuce gona da iri domin a kwanakin baya sun biya kudin fansa naira miliyan 15 da wadanda suka sace shi suka nema.
Wanda aka kashe wanda ke gudanar da wani gidan mai a Utuh, an yi garkuwa da shi kuma aka sake shi watannin baya.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar Yan sanda, Ikenga Tochukwu, ya ce;
“An sace wanda aka kashe da misalin karfe 10:15 na dare a gidansa a ranar 9 ga watan Yuni, 2022 kuma ana kokarin kubutar da shi kafin wannan mummunan lamari. An tsinci gawarsa a tsakanin iyakar Uke da Ukpor. Har yanzu ba mu ja da baya kan bincikenmu ba domin za mu tabbatar da cewa masu laifin za su fuskanci fushin doka."
Wannan lamari dai ya zo ne wata guda bayan da aka yi garkuwa da Okechukwu Okoye, dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Gwamna Chukwuma Soludo a Majalisar dokokin jihar, inda daga bisani aka same shi an sare kansa.