Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubutawa Majalisar Dattawa wasika yana neman a tantance sunayen Ministoci bakwai.
Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu, Godswill Akpabio da Emeka Nwajiuba wadanda duk suka yi murabus don neman takarar shugaban kasa ba za su koma Majalisar Ministocin shugaba Buhari ba kamar yadda aka tabbatar a cikin sabon jerin sunayen.
Wadanda aka nada sune: Henry Ikechukwu – Jihar Abia, Umana Okon Umana – Jihar Akwa-Ibom; Ekuma Joseph – Jihar Ebonyi; Goodluck Nana Obia – Jihar Imo; Umar Ibrahim Yakubu – Jihar Kano; Ademola Adewole Adegorioye – Jihar Ondo; Odo Udi – Jihar Ribas.
Majalisar Dattawa, duk da haka, ba ta tsayar da ranar da za a gudanar da aikin tantancewar ba tukuna.