Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo cewa zancen ya fito ne daga bakin Ministan shari'a kuma babban Lauyan Gwamnatin Najeriya Dr. Abubakar Malami SAN yayin da yake jawabi a wajen taron magoya baya, Yan uwa da abokansa na arziki da aka shirya a dakin taro na Gesse Otal a Unguwar Gesse da ke garin Birnin kebbi ranar Asabar 25 ga watan Yuni 2022.
Malami ya ce:
"Muna gudanar da tuntuba da zai sa kashi 60 na yan jam'iyar PDP su canja sheka zuwa jam'iyar APC cikin yan kwanaki masu zuwa insh Allah".
Malami ya kara da cewa hadakarsu na nan daram tare da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu Ya kuma bukaci kungiyoyi fiye da 600 da ke goyon bayansa su zabi APC. Ya ce yan kungiyoyin su kokarta su mallaki katin zabe PVC kafin lokacin zabe.
Ku biyo mu don karin bayani.....
SANARWA
Yadda za mu taimaka maka a fagen siyasarka ko kasuwancinka.
* Ko Ina a Duniya ana samun shafinmu na isyaku.com
* Muna da subscribers Miliyan 8
* Muna cikin group na WhatsApp guda 447
*Muna da group namu na kampaninmu na isyaku.com guda 22.
* Muna aiki ne karkashin kampani mai cikkken rijista da CAC Seniora int'l Ltd RC1470216.
* Rijistar da kowane gidan Jarida ta yi a Najeriya shi ne muka yi.
* Za mu iya tallata maka kasuwancinka ko siyasarka ta hanyar ingizon yanar gizon zamani.
* Kada sunan isyaku.com ya sanyaya maka guiwa a jaridance, sunan Jarida ra'ayi ne.otocin Honda, Toyota, Mitsubishi, Mercedes duk sunayen mutane ne.