INEC ta baiwa Atiku, Tinubu, Kwankwaso mako 1 su mika mata sunayen mataimakansu


Hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC ta bayyana ranar karshe ga jam'iyyun siyasa na mika mata takaran shugaban kasa da mataimakansu.

Hukumar tace nan da ranar Juma'a, 17 ga watan Yuni misalin karfe 6 na yamma, za'a rufe karbar sunan.

Amma na gwamnoni da yan majalisar dokokin tarayya, an basu nan da ranar 15 ga watan Yuli, 2022.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan a ganawarsa da kwamishanonin INEC na jihar REC ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Yace:

"Yau Alhamis, 9 ga watan Yuni, 2022 ne ranar karshen gudanar da zaben fidda gwanin dukkan jam'iyyun siyasa."

"Cikin mako daya fari daga gobe 10 ga Yuni, 2022, dukkan jam'iyyu zasu aika sunayen yan takaransu (Shugaban kasa/Mataimakisa, Sanatoci da majalisar wakilai) zuwa ranar Juma'a, 17 ga Yuni, 2022."

Farfesa Yakubu ya kara da cewa su kuma Gwamnoni da yan majalisar dokokin tarayya, nan da ranar 15 ga Yuli, 2022.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN