Yadda aka tsinci gawar wata mata a Abuja ya tada hankalin mutane


Mazauna Kubwa, wani gari da ke karƙashin babban birnin tarayya Abuja sun shiga yanayin kaɗuwa ranar Litinin biyo bayan abun da suka gano a wata Bola.

Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen garin sun tsinci gawar wata mata da aka daddatsa tare da gwarwakin wasu dabbobi biyu kusa da ita a bayan gadar PW, lamarin da ya tayar musu da hankali.

Gawar dabbobin, Akuya da kuma Kare a cikin buhuna daban-daban an tsince su a bayan gawar matar, wacce aka raba sassan jikin ta zuwa gida Tara.

Bayanai sun nuna cewa kowane sashi na jikin matar na nan yadda yake amma ban da gaɓar hannun ta, shi ne ake ganin an cire.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Wani mai gadi da ke aiki a ɗaya daga cikin wuraren kasuwancin mutane kusa da wurin da abun ya faru, ya ce sun wayi gari ne suka ga gawar matar wacce aka yi gunduwa gunduwa da ita.

Shugaban caji Ofis ɗin Kubwa, DPO, CSP Abubakar Abdulkarim, ya tabbatar da lamarin mai ɗaure kai da ake zargin yana da alaƙa da yan ƙungiyar Asiri.

Jami'in hukumar yan sandan ƙasar nan ya ce a halin yanzun sun fara gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar matar ta wannan halin.

Da yake tabbatar da lamarin a rahoton Punch, Kakakin yan sandan FCT Abuja, Omotayo Oduniyi, ya ce:

"A yanzun ba zamu tabbatar da zargin wasu mutane da ke ganin lamarin ya shafi yan asiri ba, mun fara bincike don gano amsoshin duk wasu tambayoyi."

Kotu ta ba da umarnin a rataye wani Magadinci har Lahira bayan kama shi da laifin kashe wani da yake zargin yana wa matarsa kwartanci.

Da take yanke hukunci, Mai Shari'a Patricia Oduniyi, ta ce Hujjojin da aka gabatar mata sun tabbatar ta laifin wanda ake zargi.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN