Yanzu-yanzu: ICPC ta kwato tsabar kudi N170m, G-Wagon, da wasu daga hannun dan kwangilar sojan Najeriya


Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ta kwato tsabar kudi har Naira miliyan 170, dala $220,965, G-Wagon da sauran kayayyaki daga hannun wani dan kwangilar soja a Abuja. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya tattaro
.

Legit.ng ta ruwaito cewa Azuka Ogugua, kakakin hukumar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a, 24 ga watan Yuni.

Ogugua ya ce bisa ga bayanan sirri, hukumar ta kai samame a wani gida da ke Wuse 2, Abuja, inda aka gano kayayyakin masu tsada.

Hukumar ta kuma karyata labarin da wasu kafafen yada labarai suka fitar na cewa ICPC ta kwato Naira biliyan 1.85 daga wani gida da ofishin da aka ce mallakin tsohon babban hafsan sojin kasa, Tukur Buratai ne a Abuja.

An kama mai gida

A cewar ICPC, kadarorin da aka kwato makudan kudaden mallakar mai kamfanin K Salam Construction Company ne, dan kwangilar soja.

Hukumar ta kara da cewa ta kama babban daraktan kamfanin, Kabiru Sallau, ganin cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.

Sanarwar ta ce:

“An jawo hankalin hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC kan wasu rahotannin da ba su dace ba, kuma gagarabadau a kafafen yada labarai game da kama wasu kudade na biliyoyin naira, daloli, agogon Rolex da aka jibge a wani katafaren gida na Abuja.

“Hukumar tana so ta bayyana cewa jami’an ICPC sun kai samame a wani katafaren gida da ke Wuse 2 na babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis 16 ga watan Yuni, 2022 tsakanin karfe 5:00 na yamma zuwa 12:00 na safe bisa zargin karkatar da kudade. a halin yanzu dai ya nuna cewa mallakar kamfanin K Salam Construction Company ne, dan kwangilar soja.

“Hukumar ta kwato kudi da sauran kayayyaki daga cikin kadarorin kamar N175,706,500; $220,965; G-Wagon; 2022 motocin BMW da Mercedes Benz, wayoyin hannu na musamman, agogon hannu masu zane da dama, da suka hada da Rolexes uku, da wasu takardun kadarorin.

“Hukumar ta kama Manajan Daraktan Kamfanin K Salam Construction Company Nigeria Limited, Mista Kabiru Sallau kuma ana ci gaba da bincike.

"Har yanzu dai hukumar ba ta kammala bincikenta ba, kuma ta gwammace kada ta yi hasashen sakamakonta sannan kuma ta kaucewa hatsaniya na shari'ar da ake yi a kafafen yada labarai."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN