Direban motar Tipa ya buge dan Acaba dauke da yar makaranta ta mutu nan take direba ya sauko ya gudu, duba abin da ya faru


 Wani abin takaici ya faru a safiyar ranar Alhamis a hanyar Zango-Lokoja, jihar Kogi, inda wata babbar mota ta buge wani babur din kasuwanci inda ta kashe fasinja, wata dalibar makarantar sakandare mai shekaru 15.

Wasu shaidun gani da ido a wurin da hatsarin ya afku sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewa wasu mutane biyu sun samu raunuka a hadarin wanda ya faru da karfe 8:00 na safe.

Wani shaidan gani da ido Mista Mike Adejoh ya ce nan take lamarin ya afku, direban motar ya gudu ya bar wadanda suka jikkata aka kwashe su zuwa asibiti.

A cewarsa, daga baya jami’an FRSC suka kai gawarwar wanda hadarin ya rutsa da ita zuwa dakin ajiyar gawa.

Ya ce bayan mutuwar dalibar, wasu gungun jama’a ne suka taru suka yi yunkurin kona motar, amma jami’an tsaro suka shiga tsakani cikin gaggawa.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan, SP William Ovye-Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce an fara gudanar da bincike kan musabbabin hadarin.

Har ila yau, kwamandan hukumar ta FRSC, Mista Stephen Dawulung, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce mutanensa sun ajiye gawar a dakin ajiye gawa na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN