Yanzu yanzu: Jami'an tsaro da Mambobin APC sun baiwa hammata iska kan tsabar kuɗi N50,000 da dan takarar shugaban kasa ya watsa a Sakatariyar APC


Direbobi, jami'an tsaro da masoyan jam'iyyar APC sun ba hammata iska kan kyautar tsabar kudi da gwamna Ebonyo. Dave Umahi, ya wurga musu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamna Umahi ya ziyarci babbar Sakatariyar APC ta ƙasa ne domin gana wa da shugaban jam'iyya, Sanata Abdullahi Adamu, kwanaki biyu bayan kwamitin da John Oyegun ke jagoranta ya tantance shi a Abuja.

Bayan gawarsu wacce ta gudana cikin sirri kuma ta shafe sama awa ɗaya, Gwamna Umahu ya amsa tambayoyin manema labarai daga nan ya nufi motarsa.

Yayin ya je gab da shiga cikin motar, Umahi ya juyo sannan ya jefa ɗaurin tsabar kudi N50,000 ga dandazom mutanen da ke wurin.

Hakan da gwamnan ya yi ya ta da yamutsi yayin da magiya bayan APC, Direbobi da jami'an tsaro suka bai wa hammata iska a kokarin samun rabon su daga kudin.

Umahi na ɗaya daga cikin yan takarar shugaban ƙasa karkashin APC guda 23 waɗn d asuka kai kansu Otal ɗin Transcorp Hilton a birnin Abuja.

Sauran yan takarar APC da aka tantance

Sauran yan takara 22 sun haɗa da, Bola Tinubu, Rotimi Amaechi, Fasto Tunde Bakare, Chukwuemeka Nwajiuba, Gwamna Muhammed Badaru, Sanata Ajayi Borroffice, Sanata Ibikunle Amosun, Ken Nnamani, da Fasto Nicholas Felix.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN