Dan Afrika ya yi marisa ya bi gari yana caka wa mutane wuka a kasar Indiya, duba yadda ta faru


Akalla mutane 8 ne suka jikkata sakamakon harin wuka da wani dan Afirka mai shekaru 50 ya kai a kudancin Mumbai na kasar Indiya. 

Ba a tabbatar da asalin wanda ake zargin ba har ya zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto kamar yadda wasu kafafen yada labaran Indiya suka bayyana shi dan Najeriya ne yayin da wasu ke cewa dan kasar Kenya ne. 

Kwamishinan ‘yan sanda na Kudancin Mumbai, Dilip Sawant ya ce lamarin ya faru ne a Lambun Tata kusa da Rijiyar Parsi da misalin karfe 4:10 na yammacin ranar Laraba, 1 ga watan Yuni. 

Jami’in ya bayyana cewa wanda ake zargin mai suna John wanda ake zargin yana cikin maye ne ya zaro wuka ya kai hari kan masu wucewa. 

An sanar da ‘yan sanda lamarin da ya faru, bayan da wata tawaga ta yi galaba a kan mutumin tare da kwace wukar daga hannunsa. 

Kimanin mutane takwas ne suka jikkata a harin a lokacin da ‘yan sanda suka isa wurin, inda daga bisani aka garzaya da su asibitin JJ da asibitin GT domin yi musu magani. 

An kai wada ake tuhumar zuwa ofishin ‘yan sanda na Azad Maidan, kuma za a shirya takardar tuhuma ta FIR a kansa. 

“Har yanzu ba a san dalilin da ya sa John ya kai harin ba, mun tsare shi kuma ana ci gaba da yi masa tambayoyi,” in ji wani jami’in ‘yan sanda na Azad Maidan. "Za a yi rajistar shari'ar yunkurin kisan kai kan wanda ake tuhuma." 

Mutane hudu da suka jikkata sun hada da: Satish Jagdambe (24), Shamal Gop (28), Anwar Khan (43) da Amin Benjamin Londhe (63), an kwantar da su a asibitin GT yayin da wasu uku - Sandeep Jadhav (36), Rohan Josheph da Raju Pardeshi. - an kwantar da su a asibitin JJ. An ce Khan ya samu munanan raunuka.

Masu bincike suna tattara bayanai game da wanda ake zargi da kuma dalilin da ya haddasa harin. Har ila yau, 'yan sandan za su duba bayanansa daga ofishin rajistar yankin baki.

Tawagar ‘yan sanda tana nazarin faifan CCTV domin gano yadda lamarin ya faru da kuma inda wadanda ake tuhumar suka fito kafin faruwar lamarin. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN