Dan shekara 20 ya yi wa matar uban gidansa da wasu mata biyu fyade bayan ya yi fashi da makamiRundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani matashi dan shekara 20 da ake zargi da yin fashi da makami, wanda ya yi wa mata uku fyade ciki har da matar ubangidansa, a ta yin batazana da wuka a karamar hukumar Musawa ta jihar.

Kakakin rundunar, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuni, ta ce wanda ake zargin, Jume Bello, ya shiga gidajen wadanda abin ya shafa a lokuta daban-daban, inda ya yi musu fyade tare da kwashe dukiyoyinsu. 

 “A ranar 31/05/2022 da misalin karfe 0900, wasu mata uku (3) daga kauyen Jikamshi, karamar hukumar Musawa, suka kawo rahoto a sashin Musawa cewa, a lokuta daban-daban, wani Jume Bello, ‘M’, mai shekaru 20 da haihuwa ya shiga gidajensu ya kai musu hari da wuka tare da yi musu fashi na kudi, wayar hannu da kuma ya tilasta musu yin jima'i da shi," in ji PPRO. 

"A cikin binciken da ake yi, an kama wanda ake zargin tare da amsa laifin da aka yi masa, ana ci gaba da bincike." Ya kara da cewa. 

A wata hira da manema labarai, wanda ake zargin ya amsa laifin yin fashi tare da yi wa matar ubangidansa, mai sayar da ruwa fyade. 

"Na kuma dauki wasu kudinta da na sauran matan, na yi amfani da wuka don tsoratar da su, na kai daya daga cikinsu a bayan gida na yi lalata da ita yayin da sauran matan ke kan gadon aurensu." Yace. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN