Buhari ya tura doguwar wasika ga gwamnonin ilahirin APC kan burin Tinubu a 2023


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC da sauran ‘ya’yan jam’iyyar su hada kai domin tabbatar da nasarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Buhari, a wata wasika da ya aike wa shugaban gwamnonin, Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi, ya ce Tinubu ba bako bane a idon gwamnonin, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar da sashen wasikar a ranar Alhamis.

A cikin wasikar, Buhari ya yaba wa gwamnan jihar Kebbi, wanda ya kasance shugaban kwamitin zaben fidda gwanin da aka kammala, bisa kwarewa da kuma yadda ya gudanar da zaben fidda gwanin cikin lumana, rahoton Blueprint.

Bola Tinubu zai daura daga inda na tsaya, Buhari

Shugaban ya ce yana fatan yin aiki da gwamnonin domin ganin Tinubu ya lashe zaben 2023.

‘’A yau a matsayina na dan jam’iyyar APC mai kishin kasa kuma mai ruwa da tsaki, na yi imanin za ku hada kai da dan takararmu domin ganin ya ci zabe a 2023.

‘’A shekaru 7 da suka gabata a gwamnati, mun samu nasarori da dama. Duk da haka, muna da abubuwa da yawa da za mu yi. Aikin APC ya yi nisa don haka muna bukatar dukkan ku da ku hada kai don ganin dorewar ci gaban tafiyarmu ta zaman lafiya da ci gaba."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN