Daga karshe: Ta karewa Ahmad Lawan, INEC ta ce Machina ya lashe zaben fidda gwani


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi watsi da batun zabo shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a zaben fidda gwani na sanatan Yobe ta Arewa.

A maimakon haka, hukumar ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin dan takara na gaskiya a jam’iyyar APC a jihar ta Arewa maso Gabas, inji rahoton PM News.

Legit.ng ta ruwaito cewa wani tabbataccen kwafin rahoton INEC daga zaben da aka gudanar ya nuna cewa Machina ya samu kuri’u 289 cikin 300 da deliget suka kada.

Rahoton ya tabbatar da ikirarin da Machina ya yi tun farko a bainar jama'a cewa shi ne ya lashe zaben fidda gwanin da aka yi kuma ya lashe tikitin takara gabanin babban zaben 2023.

Takardar da INEC ta tabbatar a ranar 23 ga watan Yuni, 2022, ta amince da takarar Machina kuma ta yi shiru gaba daya game da sunan Sanata Lawan a cikin 'yan takara.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN