Hukumar Kwastam a Kebbi ta kama fatun jakuna 2,820 wanda kudinsu ya kai N48m


Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) a jihar Kebbi ta kama fatun jakuna 2,820 wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 48. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya tattaro.

NAN ta ruwaito cewa Kwamandan rundunar hukumar a jihar Kebbi Mista Joseph Attah ne ya bayyana haka a Birnin Kebbi ranar Juma’a a lokacin da yake mika fatun jakunan ga jami’an hukumar kula da ayyukan noma ta Najeriya.

Ya ce an kama su ne bisa sahihin bayanan sirri a ranar 2 ga watan Yuni da misalin karfe 4:00 na safe a kusa da Bahindi-Dogon Rimi a karamar hukumar Bagudo.

Kwamanda Attah ya ce:

“Binciken da aka yi ya sa  an gano buhunan jumbo guda 94, kowanne yana dauke da guda 30, wanda adadinsu ya kai fatun jakuna 2,820, wanda darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 48.1,” inji shi.

Attah ya bayyana cewa cinikin fatun jakuna haramun ne, saboda ya sabawa tanadin sashe na 63 (b) na CEMA CAP C. 45, Dokokin Tarayyar Najeriya, 2004 (kamar yadda aka gyara).

“Wannan matakin farautar da aka yi ta hanyar yanka jakuna 2,820 ba abin yarda ba ne. Idan aka ci gaba da yin haka, jakuna za su bace.

“Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar kasuwanci ta kasa da kasa kan ci gaban kasa da kasa (CITES), wadda ta haramta fataucin fatar jaki.

Ya kara da cewa, “Saboda abubuwan da suka gabata, an mayar da kayayyakin zuwa kwace kamar yadda umarnin shugaban hukumar kwastam, Kanal Hameed Ibrahim Ali (rtd) ya bayar.

Ya ce mika buhunan fatun jakunan guda 94 na fatun jakuna ga hukumar kula da ayyukan noma ta Najeriya, ya kasance a cikin ruhin hadin gwiwa tsakanin hukumomin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN