Type Here to Get Search Results !

An biya Yan bindiga kusan N400m cikin shekara 2 a Birnin Gwari kafin su bari a yi noma - Dan masani


Wani Dan Majalisar Masarautar Birnin Gwari, Danmasani Birnin Gwari, Zubairu Abdulra’uf, ya ce an biya Yan bindiga N400 cikin shekaru biyu da suka gabata kafin manoma su sami sukunin noma da girbe amfanin gonarsu. Shafin isyaku.com ya samo.

Tsohon babban Daraktan hukumar watsa labarai na jihar Kaduna, Kaduna State Media Corporation, ya gayawa manema labarai a Kaduna lokacin wani ganawa ranar Alhamis 30 ga watan Yuni.

Ya ce:"  An biya Yan bindiga N200m a gundumar Randegi kadai. Idan ka yi maganar karamar hukumar Birnin Gwari gaba daya, an biya tsakanin N300m zuwa N400m".

Ya ce an biya kudaden  ne a matakai daban daban da suka hada da kafin lokacin noma, tsakiyar damana da kuma karshen damana lokacin girbe amfanin gona.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies