Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kashe dan sanda a shingen bincike tare da kone motar sintiri a jihar Enugu


Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wasu shingen binciken jami’an ‘yan sanda guda biyu a Nsukka, karamar hukumar Nsukka ta jihar Enugu, inda suka kashe jami’i guda tare da kona wata motar sintiri. 

Kafar Labarai na yanar gizo isyaku.com ya tattaro cewa an kai harin ne da sanyin safiyar Juma’a, 17 ga watan Yuni. 

An kashe dan sandan ne a mahadar Umaru da ke Nsukka yayin da aka kona motar ‘yan sanda a kan titin Ibeagwa-Ani.

Wani ganau ya shaida wa NAN cewa mazauna yankin sun ji karar harbe-harbe da misalin karfe 6:20 na safe. Bayan haka, sai suka garzaya zuwa mahadar, suka tarar da dan sandan da ba shi da rai a kasa.

“Na garzaya zuwa kofar gidana don tabbatar da cewa dukkansu suna cikin kulle sosai, na kashe duk fitulun wutar da ke gidana na ce mata ta da ‘ya’yana su yi shiru domin ina ganin ‘yan fashi da makami ne,” inji shi.

Ya ce bayan harbe harben ya tsaya ne ya bi sahun mutanen da suka garzaya zuwa mahadar inda ya tarar da gawar dan sandan a kasa.

“Sun ce an kashe dan sandan ne a yayin wani artabu tsakanin ‘yan sandan da ke shingen bincike da ‘yan bindigar,” inji shi.

Wani dan kasuwa da ya shaida lamarin a hanyar Ibeagwa zuwa Ani inda aka kona motar ‘yan sanda ya ce yana cikin wata motar bas ta kasuwanci da ke zuwa kasuwar Nkwo Ibeagwa-Ani sai suka hango motar ‘yan sanda ta kone tare da wasu mutane biyar dauke da makamai wadanda suka rufe fuskokinsu suna kallon motar yayin da take ci ta wuta.

Kakakin hukumar yan sandan jihar  Daniel Ndukwe ya tabbatar da faruwar lamarin. 

" Mun sami rahoton farmaki da aka kai wa jami'an mu yau a Nsukka, amma lamarin bayanan na da sarkakiya a halin yanzu" a cewarsa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN