Yanzu yanzu; Tinubu ya zabi abokin takararsa, duba suna da jiharsa

Rahotanni sun bayyana cewa Tinubu ya zabi abokin takararsa.


A wani yunkuri na doke wa’adin da INEC ta bayar na mika dan takarar, APC ta mika sunan abokin takarar Bola Ahmed Tinubu. Sunan da aka mika shine Alhaji Kabir Ibrahim Masari, dan asalin jihar Katsina wanda yayi aiki a zamanin tsohon shugaban kasa Ya'adua Dan siyasar haifaffen Katsina, mamba ne a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabarun (NIPSS). 

An bayyana Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin takarar Asiwaju Bola Tinubu , dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, gabanin babban zabe na 2023. Masari mamba ne a hukumar kula da manufofi da tsare-tsare ta kasa (NIPSS) dake Kuru kusa da Jos, babban birnin jihar Filato, inji rahoton AIT .

Kamar yadda Aminiya ta tattaro , Tinubu ya mika sunan Masari a matsayin wanda zai tsaya gabanin wa’adin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na jam’iyyu su mika sunayen ‘yan takararsu a zaben 2023. 

A cewar jaridar, an tabbatar da faruwar lamarin ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuni, ta hannun wasu makusantan Tinubu da Masari. 

Sai dai wasu rahotanni na cewa Tinubu wanda ya mika sunan Masari ne kawai domin ya doke hukumar zabe ta INEC, zai maye gurbinsa kafin zaben shugaban kasa na 2023.
Hakan dai na zuwa ne bayan jam’iyyar APC ta kammala shirye-shiryenta da tuntubar juna kan wanene ainihin mataimakin Tinubu. 

Hakan dai na zuwa ne bayan jam’iyyar APC ta kammala shirye-shiryenta da tuntubar juna kan wanene ainihin mataimakin Tinubu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN