An fitar da jerin sunayen kwamandojin kungiyar IS da ke yammacin Afirka (ISWAP) da sojoji suka bindige.
An kashe kwamandojin ne a wani samame da sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami'an hadin gwiwa na kasa da kasa suka kai makonnin da suka gabata.
Rahotanni sun ce sojoji sun kutsa cikin sansanin ‘yan ta’addan, wanda ke dauke da mayakan kungiyar Boko Haram fiye da 3,000 na bangaren Abubakar Shekau. Hakan ya haifar da fafatawa da bindiga wanda ya shafe sama da awanni 3 ana gwabzawa.
Wata majiya ta shaida wa Daily trust cewa;
"An kama ‘yan ta’adda biyu da ransu. A lokacin da suke ba da shaida, sun yi ikirari cewa sansanin na karkashin jagorancin wani babban kwamandoji ne a karkashin wani Abu Ikilima. An kashe Khayd uku (hakimai), Munzul uku (kwamandan hafsoshi), 1 Nakib (kwamandan) na Boko Haram da kuma wasu mayakan da dama.”
A cikin wani faifan bidiyo da kungiyar ISIS ta fitar, an jera sunayen kwamandojin ISWAP da aka kashe kamar haka;
Abu Musab al-Yobawi
Abu Nu'man al-Amni
Abu Abdullah al-Barnawi
Abu Ammara al-Barnawi
Abu Anas al-I'alami
Abdul Malik al-Barnawi
Abu Sufyan al-I'alami
Shaykh Abu Bakr al-Da'wi
Abu Usama Goneri
Abu Sa'ad al-Ansari
Abu Jabbar al-Barnawi
Abu Anas al-Barnawi
Abu Abdul Rahman al-Katsanawi
Abu Maryam al-Gidami
Abu Salman al-Ansari
Baka Goneiri
Abu Mustafa al-Askari
Farooq al-Barnawi
Abu Ahmad al-I'alami
Al-Qassim Al-Barnawi
Mustafa al-Barnawi
Abbas al-Ansari
Musa al-Ansari