Da dumi-dumi: Shugaban Majalisar Dattawa Yahaya Abdullahi ya fice daga APC zuwa PDP a jihar Kebbi


Shugaban majalisar dattawa kuma dan majalisa daga jihar Kebbi, Sanata Yahaya Abdullahi ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress APC zuwa jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP.

Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Muhammad Jamil Gulma ya tabbatar da hakan. Vanguard ta ruwaito cewa; 

“Shugaban majalisar dattijai Dakta Yahaya Abdullahi a ranar Laraba da karfe 9 na safe zai bar Abuja zuwa Kebbi ya wuce karamar hukumar Kamba domin shelanta komawarsa jam’iyyar PDP da kuma nuna sha’awarsa ta tsayawa takara a yanzu.”

Yahaya wanda tun da farko ya shiga zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kebbi na jam’iyyar APC, bai sami kuri'a ko daya ba, sakamakon da ya ki amincewa da shi, ya kuma bayyana shi a matsayin abin kunya da wasan yara.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN