Da dumi-dumi: EFCC na aikin sirri wajen zaben fidda gwani na APC Inji Majiya, duba dalili


Wata majiya mai karfi a Hukumar Yaki da Rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta tabbatar da cewa jami'an hukumar na aikin sirri wurin lura da deliget tare da kiyaye yadda ake siyan kuri'u a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC mai mulki. 

Majiyar abin dogaro, wacce ta yi magana da Punch kan a boye sunanta, ta ce, "A halin yanzu muna filin zaben fidda gwani a sirrance. Muna lura kuma muna kallon yadda ake cusawa deliget ra'ayi, ake siyan kuri'u da sauran magudin zabe na kudi da ka iya faruwa."

Majiyar ta tabbatar da cewa, hukumar EFCC na aikin sirrin domin kama mahandama ta hanyar yi musu ba-zata.

Wannan rahoton na zuwa ne bayan batun da ke yawo na cusawa deliget $40,000 wanda manyan 'yan takara ke badawa.

Kwana goma cif da ta gabata kenan da jami'an hukumar EFCC suka dira filin wasa na Mashood Kashimawo Abiola da ke Abuja yayin da ake gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP.

Jami'an sun dira wurin karfe 4 na yamma.

An gano cewa, jami'an sun dira filin zaben ne bayan rahoton siyan kuri'u da cin hanci da ake bai wa deliget ya watsu.

A yayin da aka nemi jin ta bakin mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ki yin tsokaci a kan hakan.

Ana taron ne a Moshood Kashimawo Abiola National Stadium a Abuja. Jami'an sun bayyana ne don sa ido a kan yadda ake shakara wa wakilan jam'iyya kudi da tare da almubazzaranci.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN