Wani Ma’aikacin gwamnati ya maka Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon Kotu saboda ta ki aurensa bayan ya kashe mata N396,000.

Wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa mai shekaru 48 a duniya ya maka fitacciyar jarumar Kannywood Hadiza Gabon a gaban kotu bisa laifinta na kin auren sa. Kafar labarai ta yanar gizo isyaku.com ya samo.

Kamar yadda NAN ta ruwaito, bangarorin biyu sun bayyana a gaban wata kotun shari’ar musulunci a jihar Kaduna a ranar Litinin 6 ga watan Yuni. 

Wanda ya shigar da karar ya shaidawa kotu cewa yana da alaka da jarumar kuma ta yi alkawarin aurensa.

“Ya zuwa yanzu na kashe mata Naira 396,000, duk lokacin da ta nemi kudi ina ba ta ba tare da bata lokaci ba da fatan za mu yi aure, ita ma ta kasa fitowa a Gusau da ke Zamfara inda nake zaune bayan na yi duk wani shiri da na yi na karbe ta,” inji Musa.

An fara sauraren karar ne a ranar 23 ga watan Mayu amma wanda ake kara bata kasance a gaban kotu. 

A nata bangaren, wanda ake kara wanda ya samu wakilcin Lauyanta, Mista Mubarak Kabir ya bayyana cewa wanda yake karewa ba ta da tabbacin sahihancin sammacin.

"Matsayin wacce nime katewa na shahararru yana jawo mutane daban-daban masu niyya daban-daban. Ta kasance mai taka-tsan-tsan game da tsaron lafiyarta," in ji Kabir.

Kabir ya roki kotu da ta kara masa lokaci domin gabatar da wanda yake karewa a kotu.

Alkalin kotun, Malam Rilwanu Kyaudai, ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yuni 2022. 

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE