Shugaban jam'iyyar All Progressive Congress wato APC, Sanata Abdullahi Adamu ya nuna damuwa kan yadda guguwar sauya sheka ta mamaye jam'iyya mai mulki.
Daily Trust ta ruwaito cewa Sanatocin APC 7 ne suka sauya sheƙa zuwa wasu jam'iyyun adawa bayan gaza samun tikitin takara a babban zaɓen 2023 da ke tafe.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar sirri da Sanatocin APC, Sanata Adamu ya ce abin takaici ne yadda yan majalisun ke barin jam'iyya mai mulki.
Ya ce dama ana tsammanin haka kasancewar yanzu ne ake ta shirye-shirye zaɓe, kuma an saba ganin irin haka na faruwa a ƙasar nan a wannan lokacin.
Shugaban APC ya ce:
"A duk shekarar zaɓe, irin haka na faruwa da mutane, masu ruwa da tsaki su shiga damuwa. Najeriya ba wata shaffafa da mai bace da hakan zata ƙi faruwa, haka ma APC."
"Sabida haka ba abin da ya shafe da kome ke faruwa a sauran jam'iyyu, na jam'iyyar mu ne kaÉ—ai yake damuna. Kun san cewa ba a AOC kaÉ—ai haka ke faruwa ba, saboda muna tsagin jam'iyya mai mulki, matsalar mu ta fi jan hankalin mutane."
Mun damu, amam zamu É—auki mataki - Adamu
Adamu ya ƙara da cewa abubuwan da ke faruwa na sauya sheka a jam'iyya mai mulki ya sa shi cikin damuwa sosai a matsayinsa na shugaba.
"Babu shugaban da ba zai shiga damuwa idan ya rasa mamba É—aya ba, ba wai biyu ko uku ba, É—aya kacal."
"A halin yanzun muna tsakiyae fuskantar damuwar ne amma ni da sauran mambobin kwamitin ayyuka mun shirya fuskantar matsalar kuma zamu warware ta idan Allah ya so."
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI