Da dumi-dumi: Magoya bayan APC da na SDP sun ba hammata iska a Ekiti an kashe mutum daya da dama sun sami rauni


Rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da na jam’iyyar adawa ta Social Democratic Party a garin Itaji-Ekiti da ke karamar hukumar Oye a jihar Ekiti ya yi sanadin mutuwar mutum daya. 

Rikicin da ya yi sanadin mutuwar dan jam’iyyar APC, Tope Ajayi, tare da raunata wasu da dama, ya faru ne a ranar Asabar 11 ga watan Yuni yayin yakin neman zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wadanda suka samu raunuka suna samun kulawa a sashin kula da lafiya na asibitin koyarwa na jami’ar jihar Ekiti da ke Ado Ekiti.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce; 

"Eh, an yi arangama a Itaji tsakanin 'yan jam'iyyun adawa kuma an fara gudanar da bincike don gano abin da ya faru da adadin wadanda suka mutu da kuma yiwuwar kama masu laifi."

Abutu ya ce, ‘yan sandan sun kwantar da al’amarin tare da dawo da zaman lafiya a garin.

Ya kara da cewa; 

“Amma kan kashe mutum, har yanzu ba mu sami tabbacin hakan ba. Da zaran an yi haka, zan sanar da ’yan jarida".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN