Jaruntakar da wani direban babbar mota ya yi ya samu karbuwa a wajen 'yan Najeriya bayan da ya yi kasada da ransa don ceto wasu.
Mutumin mai suna Mista Ejiro Otarigho, ya tuka wata babbar mota da ke cin wuta daga wani unguwar da jama’a ke da yawa a garin Agbarho da ke Ughelli ta Arewa a jihar Delta, zuwa wani yanki da babu yawan jama’a domin rage barnar da za ta yi idan ta fashe.
A cikin wani faifan bidiyo da aka yada ta yanar gizo, an ga direban yana tuka motar, bai damu da hadarin fashewa ba. Ya tuka ta zuwa wata hanyar daji babu gidaje da shaguna a kusa.
Ya fito daga cikin motar da ta kone da ransa. Ba a rasa rai ba.
'Yan Najeriya sun shiga shafin Facebook suna jinjina masa tare da gode masa.
Kalli bidiyo a kasa...