Yanzu-Yanzu: Ba za a kakabawa APC dan takarar shugaban kasa ba, inji Buhari


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba za a kakaba dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa ba, TheCable ta ruwaito

A cewar wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa Buhari ya fitar, Buhari ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wani taro da gwamnonin APC na yankin Arewa suka yi.

Kalaman shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya amince da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar.

A cewar sanarwar:

“An zabe ka kamar yadda aka zabe ni. Ka zama mai hankali kamar yadda nake. Allah ya bamu dama; ba mu da dalilin korafi. Dole ne mu kasance a shirye don daukar zafi kamar yadda muke daukar farin ciki. A bar wakilai su yanke shawara. Dole ne jam’iyyar ta shiga, babu wanda zai nada kowa.”

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE