An gurfanar da yar aikin gida a gaban Kotu bisa zargin satar takalmi mai darakar N500.000 na diyar mai gida


Wata mata ‘yar shekara 37 mai suna Aisha Salisu a ranar Talata ta tsaya a gaban wata kotun karamar hukumar Karu a Abuja, bisa zarginta da satar takalman da darajarsu ta kai N500,000.

Lauyan masu gabatar da kara, Ade Adeyanju ya shaidawa kotun cewa takalmin diyar maigidan Salisu ne.

Aisha na titin Kaduna a Niger ta tsaya ne bisa zargin sata.

Lauyan masu shigar da kara, Ade Adeyanju ya shaida wa kotun cewa wani Jude Duru ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Maitama, Abuja a madadin wanda ya ke karewa, Hajia Amina Fodio.

Adeyanju ya yi zargin cewa wanda ake zargin ta shiga dakin Fodio ne ta sace takalmin da ya kai Naira 500,000.

Ya ce laifin ya ci karo da sashe na 289 na kundin laifuffuka.

Sai dai wanda ake tuhumar ta musanta aikata laifin.

Alkalin kotun, Mista Hassan Mohammed ya shigar da karar wanda ake tuhumar da bayar da belinta a kan kudi N500,000 tare da mutane biyu da za su tsaya mata.

Mohammed ya ba da umarnin cewa wadanda za su tsaya mata dole ne su bayar da hanyar tantancewa sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 22 ga watan Yuni.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN