Babbar magana: Wani Kafinta ya yi wa matar aure duka ya yayyaga mata tufafi, duba abin da ya biyo baya


Wani kafinta mai shekaru 30, Bola Omotehinse, a ranar Larabar da ta gabata ya gurfana a gaban wata Kotun Majistare dake Okitipupa a jihar Ondo, bisa zarginsa da lakada wa wata uwar gida mai suna Bukola Adeogun duka. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.

NAN ta ruwaito cewa Omotehinse, wanda ba a bayar da adireshinsa ba, yana fuskantar tuhuma biyu da suka shafi aikata laifuka da kuma cin zarafi.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Zedekiah Orogbemi, ya shaidawa Kotun cewa wanda ake karar, a ranar 4 ga watan Yuni da misalin karfe 09:00 na safe. A tsohon gareji, Okitipupa, ya yayyage tufafin mai matar.

Orogbemi ya bayyana cewa an fara samun matsala ne biyo bayan wata ‘yar karamar gardama tsakanin mai kara da wanda ake kara kan rashin biyan tsohon bashinsa bayan ya yi aiki.

Mai gabatar da kara ya ce wanda ta shigar da karar ta samu raunuka iri daban-daban sakamakon bugun da aka yi mata, inda ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 516 da 451 na kundin laifuffuka, Cap.37, Vol. 1, Dokar Jihar Ondo, 2006.

Sai dai wanda ake tuhumar ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Alkalin kotun, Mista Chris Ojuola, ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N100,000, da kuma wanda zai tsaya masa.

Ojuola ya kara da cewa wanda zai tsaya masa dole ya kasance mazaunin da ke karkashin ikon kotun, sannan kuma dole ne ya nuna shaidar biyan harajin shekara biyu ga Gwamnatin jihar Ondo.

Daga nan sai ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 12 ga watan Yuli

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN