Da dumi-dumi: An bayyana irin salon kisan da za a dinga yi wa Yan bindiga da masu garkuwa a Zamfara


Gwamna Bello Matawalle, a ranar Talata, ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka ta yaki da yan bindiga da laifuka masu alaka a jihar.

A karkashin dokar, wacce ta fara aiki nan take, ta tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk dan bindiga da laifuka masa alaka da hakan a Zamfara

Da ya ke jawabi jim kadan bayan rattaba hannu kan dokar, Matawalle ya ce dokar na cikin matakai ne na yaki da yan bindiga, masu garkuwa da satar shanu a Zamfara.

Majalisar Dokokin Jihar ta Zamfara ta amince da kudirin dokar ne a ranar Litinin 27 ga watan Yunin 2022.

Matawalle ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa a karkashin doka don kare mutanen jiharsa.

"Za mu cigaba da bibiyan hanyoyin samar da tsaro a Zamfara a karkashin mulki na.

"Ya kamata wadanda ke sukar matakan da na dauka don samar da tsaro su yi la'akari da halin da muke ciki na hare-haren yan bindiga.

"Su duba mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da aka kashe wa, raunatawa da garkuwa da su a kullum a sassa daban na jihar," in ji shi.

Gwamnan ya ce jami'an tsaro masu kare unguwanni ba su da banbanci da dakarun JTF na Borno da Amotekun a kudu maso yamma.

Ya ce sabuwar dokar za ta bada daman hukunta wadanda aka samu da hannu wurin hare-haren yan bindiga da laifuka masu kama da su a karkashin doka.

"Duk wanda aka samu da laifin harin yan bindiga, garkuwa, satar shanu, kungiyar asiri ko yi wa yan bindiga leken asiri zai fuskanci hukuncin kisa," ya kara.

Ta kuma bada damar yanke hukuncin daurin rai da rai, daurin shekaru 20 ko 10 ba tare da zabin biyan tara ba ga wanda aka samu yana taimakawa masu aikata laifi.

Matawalle ya yaba wa majalisar jihar don jajircewa wurin yin aikinsu na doka

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN