An kama wasu sojoji biyu da ke samun horo a runduna ta 155 masu sulke da ke Damongo a yankin Savannah na Ghana, bisa zargin yi wa wata dalibar Kwalejin horar da ma’aikatan jinya ta Damongo fyade.
Citi News ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na daren Lahadi, 12 ga watan Yuni, inda wadanda ake zargin suka je makarantar domin ganawa da wata kawarsu.
Dalibar ta fito daga daki dauke da takardunta na karatu, sai sojin suka ja ta bisa zaton cewa mawarsu ce suka ja ta zuwa wani rami suka yi mata fyade. An kai rahoto ga rundunar sojin da ke Damongo lamarin da ya faru, inda aka gudanar da faretin tantance mutane tare da gano mutanen biyu.
Daga bisani an mika su ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike. Za a gurfanar da sojojin biyu a gaban kotun gundumar Bole a ranar Talata 14 ga watan Yuni.