Wani mutum ya kashe kanshi saboda budurwarsa ta auri wani, ya mutu yana rike da katin daurin aurenta (Hotuna)Wani mutum dan shekara 42 mai suna Ibrahim Adamu Mohd ya kashe kansa ta hanyar rataya a unguwar Kanti da ke karamar hukumar Kazaure a jihar Jigawa bayan budurwarsa ta auri wani mutum. 

An tattaro cewa mazauna garin Kanti sun wayi gari a safiyar Lahadi, 12 ga watan Yuni, inda suka tarar da mutumin da igiya a wuyansa, ya rataye a jikin bishiya.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, ya ce marigayin dan asalin kauyen Gayawa ne da ke karamar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano.

Ya ce Ibrahim ya kashe kansa ne ta hanyar rataya a kan titin Daura Road hannun riga da Baushe a garin Kazaure a wani gini da ba a kammala ba.

Kakakin na Hukumar Yansanda ya ce an samu katin gayyatar aure da katin SIM guda biyu a hannun mamacin. 


Da yake zantawa da Premium Times, kakakin ‘yan sandan ya ce katin gayyata na budurwarsa ne. 

Ya ce iyalan mutumin sun tabbatar da cewa mutumin ya kashe kansa ne saboda ya ji rauni bayan budurwar tasa ta auri wani mutum. 

Adam ya ce marigayin ya yi tattaki ne daga makwabciyarsa Kano domin kashe kansa a yankin, inda ya ce a dalilin haka ne mazauna unguwar suka ga gawarsa a rataye a jikin bishiyar ba su gane shi ba.

Tuni dai aka ajiye gawar marigayin a dakin ajiye gawa na karamar hukumar Kazaure

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE