Kwankwaso: Ni zan magance matsalar rashin tsaro, na daidaita tsarin ilimi bayan mulkin APC


Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP Engr Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro da samar da ingantaccen ilimi a kasar idan ya zama shugaban kasa.

Tsohon ministan tsaro kuma gwamnan jihar Kano, ya kuma ce zai bullo da kyawawan manufofin tattalin arziki da za su ciyar da kasa gaba, Leadersip ta ruwaito.

Kwankwaso ya yi wannan alkawarin ne a jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi a cibiyar Kolanut, a wata ganawa da wakilan jam’iyyar NNPP a Calabar.

Ya bayyana cewa zamansa a fadar shugaban kasa, rashin tsaro da ya addabi al’ummar kasar a ‘yan kwanakin nan, zai zama tarihi.

Ya ba da tabbacin samar da ingantaccen ilimi da ingantattun tsare-tsare na tattalin arziki da za su taimaka wajen raya arzikin kasa, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya na gida da na kasashen waje da su hada kai wajen zaben sa a matsayin shugaban kasa.

A kalaman Kwankwaso:

"Zan magance matsalar rashin tsaro, na samar da ilimi mai inganci da ingantattun tsare-tsare na tattalin arziki da za su iya daga al'ummar kasar zuwa kan tudun mun tsira."

A jawabinsa na farko shugaban NNPP na jihar Kuros Riba, Tony Odey, ya bayyana cewa zaman Kwankwaso a kan kujerar shugaban kasa, matsalar rashin tsaro za ta zama tarihi.

Ya kuma bukaci kowa da kowa ya tashi tsaye domin ganin Kwankwaso ya zama shugaban kasa, inji Daily Sun.

A cewarsa:

“Najeriya za ta samu idan aka zabi Kwankwaso. Duk da cewa an mayar da Siyasar Najeriya ta zama wasa da daloli, mun samu wani fitaccen mai gina kasa, wato Engr. Rabiu Kwankwso.

“Kwankwso ya zo da kwarin gwiwar da muka cancanta.

"Najeriya na muradin ganin sauyi kuma mutum daya tilo da zai iya haifar da wannan sauyi shine Kwankwaso."

“Ya yi yaki da rashin tsaro a lokacin da yake mulki a matsayin gwamnan jihar Kano ba tare da zubar da jini ba. Ina ganin idan muka ba shi dama zai iya yin irin haka a shugabancin Najeriya.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN