Labarai ke fitowa daga jihar Zamfara na cewa matar shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya NULGE reshen jihar Zamfara da aka sace a unguwar Damba da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara, ta haihu a sansanin ‘yan bindigar. Shafin isyaku.com ya ruwaito.
Ramatu Yunusa tana da ciki wata tara a lokacin da aka sace ta.
Mijinta, Mista Yunusa, ya ce ta haifi jaririnsu ne da misalin karfe 3 na safiyar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022, a sansanin ‘yan fashin.
Ya ce ko da an hana shi ganin matarsa da jaririyar.
Ya ce: "Kamar yadda nake magana da ku yanzu, ban sani ba ko jaririn da aka haifa namiji ne ko yarinya amma abin da na sani shine matata ta haifi jaririn."
Ramatu Yunusa, ma’aikaciyar jinya ce a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Gusau, an sace ta ne da sanyin safiyar Talata, 28 ga watan Yuni, 2022, a gidanta da ke Damba a Gusau.
Rubuta ra ayin ka