Wasu gungun birai sun kashe wani jariri da suka sace shi daga hannun mahaifiyarsa a lokacin da take shayar da shi. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya tattaro.
Jaririn dan wata daya yana tare da mahaifiyarsa a wajen gidan dangi a wani kauye a Tanzaniya lokacin da abin takaici ya faru, in ji 'yan sanda. Yaron ya ji rauni a kansa da wuyansa kuma ya rasu a lokacin da ake jinyar gaggawa.
Kwamandan yankin James Manyama ya ce mutanen kauyen sun yi kokarin yin amfani da karfi a yunkurin ceto Luhaiba daga hannun biran.
Daga nan ne dabbar ta caccaki yaron tare da kashe shi, kamar yadda jaridar kasar Tanzaniya The Citizen ta ruwaito.
Mista Manyama ya ce: "Ta yi kururuwa don neman taimako, mutanen kauyen sun garzaya gidanta don taimaka mata wajen ganin an dawo da yaronta - mai suna Luhaiba Sa'id daga hannun birai.
'Lokacin da suka yi kokarin mayar da shi da karfi sai ya ji rauni a kai da kuma wuyansa.'
'Yan sanda sun bukaci 'yan kasar da su ci gaba da lura da dabbobi masu hadari.
Kwamandan ya kara da cewa: ''A lura cewa kauyen Mwamgongo yana da iyaka da dajin Gombe mai cike da dabbobi masu hadari.
'Al'amarin dabbobi na mamaye kauyuka ba bakon abu ba ne.'