2023: Tashin hankali a PDP yayin da mambobi 10,000 suka canja sheka zuwa APC


Akalla mambobin jam’iyyar PDP 10,000 ne aka bayyana cewa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Osun a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa, an yi wannan biki na sauya sheka ne a filin shakatawa na Nelson Mandela da ke Osogbo, babban birnin jihar.

Legit.ng ta tattaro cewa Hon Wale Ojo, shugaban tsagin PDP na jihar, da Hon Albert Adeogun, dan takarar mataimakin gwamnan PDP a zaben 2018 a Osun, na daga cikin wadanda suka fice daga PDP zuwa APC.

Wasu fitattun sunayen da suka koma jam’iyyar APC mai mulki su ne tsohon dan majalisar wakilai; Ayodele Asalu (Asler), dan takarar majalisar wakilai a mazabar tarayya ta Ede da kuma Soji Ibikunle, kusan jam'iyyar.

An kuma bayyana cewa adadin wadanda suka sauya sheka ya karu a unguwanni daban-daban, kananan hukumomi da kuma mazabun tarayya na jihar.

Ficewar ta zo ne makonni kadan bayan gudanar da zaben gwamna a jihar Osun.

Osun 2022: Dalilin da ya sa muka sauya sheka daga PDP zuwa APC – Wale Ojo

Da yake magana a madadin wadanda suka sauya shekar, Honarabul Wale Ojo ya danganta matakin sauya shekar zuwa jam’iyya mai mulki da bukatar samun daidaito da wata alama ta nagarta da ci gaban Gwamna Oyetola.

Yace:

“Shiga jam’iyyar adawa a Osun tamkar hada karfi da karfe ne da mabarnata. Jam'iyyun da suka gaji asara a jere ba su da darajar da ta cancanta a bi ta ga duk mutumin gaske kuma mai hango jagoranci mai kyau.

"Don haka ne muka zo mu daidaita da alamar daukaka da ci gaba na gwamna Oyetola."

Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan PDP Adeogun ya yaba wa Oyetola

A nasa jawabin, Albert Adeogun, dan takarar mataimakin gwamna a jam’iyyar PDP a zaben 2018, ya yaba wa Oyetola bisa yadda ya kawo kwanciyar hankali a rigingimun siyasar jihar, inda ya kara da cewa zaben Oyetola daidai yake da ‘yantar da jama’a.

A kalamansa:

“A yau mun zo ne domin mu hada kai da jam’iyya mai ci gaba don ba da gudummuwa ga gagarumin aikin da ake yi. Muna jinjina wa gwamnan, wanda duk da karancin kudi a jihar ya ci gaba da tafiyar lamurra daidai.

“Lokacin da muke ‘yan adawa, muna da sakonnin gangami masu karfi a kan APC, amma Oyetola ya ji da duk wadannan batutuwa kuma ya kashe dafin PDP. Ya kamata a sanar da kowani dan kasa kuma a fahimtar da shi cewa zaben Oyetola kuri’ar ‘yanci ce."

Omisore ya karbi wadanda suka sauya sheka

Da yake karbarsu zuwa cikin jam’iyyar, Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Iyiola Omisore, ya yi maraba da wadanda suka sauya sheka bisa daukar matakin da ya dace na shiga cikin jirgin ci gaban gwamnatin jihar.

Omisore ya bayyana zabin nasu a matsayin abu mai daraja da kuma tunani mai kyau, sun dawo cikin iyali da ke samar da yanayi na daidaito da adalci.

Da yake jawabi ga wadanda suka sauya sheka da kuma amintattun jam’iyyar, Gwamna Adegboyega Oyetola, ya yabawa sabbin ‘yan mambobin bisa daukar kwakkwaran mataki na inganta siyasarsu, yana mai cewa APC ta yi fice wajen yin adalci.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN