Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) Alhaji Sa’ad Abubakar III ya umarci al’ummar Musulmi da su duba ganin jinjirin watan Dhul-Hijja daga ranar Laraba 29 ga watan Yuni. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, Shugaban kwamitin shawarwari kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi, Sarkin Musulmi ya kuma yi addu’ar Allah ya taimaki al’ummar Musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini.
Sanarwar ta ce;
“Ana sanar da al’ummar Musulmi cewa ranar Laraba 29 ga watan Yuni, daidai da 29 ga Zul-Qidah 1443AH, ita ce ranar da za a duba jinjirin watan Zul-Hijjah 1443AH.
"Saboda haka an bukaci Musulmai da su fara neman jinjirin wata a ranar Laraba kuma su kai rahoto ga gunduma ko kauye mafi kusa don sadarwa ga Sarkin Musulmi."