Bayanai sun kara bayyana kan dalilin da yasa 'dan takarar shugabancin kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi watsi da mika masa sunan gwamnan Ribas, Nyesom Wike da aka yi kan ya zama abokin tafiyarsa a zaben 2023.
Atiku a ranar Alhamis ya gabatar da gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin wanda ya zaba su yi tafiyar tare, kwanaki 18 bayan tsohon mataimakin shugaban kasar ya ci zaben fidda gwani na 'dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP, karo na biyu a jere.
Wike, wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwanin, yana daya daga cikin gwamnoni uku da 'yan kwamitin wucin-gadi na PDP suka bukaci Atiku ya duba a matsayin abokin tafiyarsa. Sauran su ne Okowa da takwaransa na Akwa Ibom, Gwamna Udom Emmanuel.
Sai dai, Atiku ya sanar da manyan shugabannin jam'iyyar cewa ba zai iya aiki da Wike ba. Baya ga kwatanta shi da yayi da abokin hamayya na kai tsaye, 'dan takarar yace Wike ba ya kaunarsa inda ya buga misali da yadda ya kusa hana shi cin zaben fidda gwani a 2018 a Fatakwal.
A wannan lokacin, Wike na goyon bayan gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, wanda daga bisani ya zo na biyu a zaben, Premium Times ta ruwaito.
A takaice dai, janyewar da Tambuwal yayi tare da bukatar magoya bayansa da su zabi Atiku suna daga cikin dalilan nasarar Atiku a zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 29 ga watan Mayu.
Bayan taron, Atiku ya ziyarci Wike a gidansa dake Abuja, inda gwamnan yayi wa 'dan takarar alkawarin goyon bayansa da jam'iyyar a zabe mai zuwa.
Kamar yadda na cikin gida a jam'iyyar ya bayyana, "Atiku ya firgita bayan Wike ya koma Fatakwal kuma a bayyane ya dinga caccakar takwarorinsa gwamnoni kan goyon bayan Atiku a zaben fidda gwanin."
Atiku ya kara sakankancewa, rikicin da ya shiga tsakanin tsohon shugaban jam'iyyar, Uche Secondus da Wike, ya biyo bayan zargin da gwamnan yayi cewa Secondus na bayan Atiku.
Kamar yadda majiya tace, dattawa da shugabannin jam'iyyar sun ji tsoron zaben Wike saboda zai tarwatsa jam'iyyar a maimakon hada kanta, inda suka ce da yawa daga takwarorinsa na kudu kudu da kudu maso gabas ba su son yadda yake gudanar da lamurransa.
"Shugabanninmu sun shaida rawar da Wike ya taka wurin farfado da jam'iyyar a yayin da take cikin wani hali, amma ba su son yadda yake takama da kuma yadda yake barazana ga jam'iyyar da shugabannin ta a kowanne lokaci.
"Sun yarda cewa irin wannan fitinannen ba zai dace da mukamin mataimakin shugaban kasa ba, hakan ne dalilin da yasa shugabannin jam'iyyar ba su goyon bayan Wike," majiyar tace.
Sakamakon karfin da Wike ya nuna a zaben fidda gwani wanda ya janyo masa goyon baya daga deliget a fadin kasar nan, magoya bayansa da shugabannin jam'iyyar suka yi kira ga Atiku da ya dauka Wike a matsayin mataimaki a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 mai zuwa.
An gano cewa, Atiku ya sha alwashin duba Okowa domin ya zama mataimakinsa don ya samu kuri'un deliget din Delta tun a wurin zaben fidda gwani.
Sai dai, bayan ana ta kira ga Atiku a jam'iyyar da ya dauka Wike, ya yi alkawarin bai wa gwamnan Ribas din ko wanda ya zaba matsayi a ma'aikatar man fetur idan ya ci zabe, sai dai gwamnan yayi watsi da hakan. Domin gujewa zargin cewa a 2019 kai tsaye ya zabi Obi, Atiku ya mika lamarin ga shugabannin jam'iyyar.
Duk da kwamitin sun zabi Wike, Atiku ya yanke hukuncin samun Wike ya sanar masa hukuncinsa amma bayan Wike ya gano Okowa Atiku ke so, ya bar garin Abuja da gaggawa.
Har yanzu dai babu tabbacin ko Atiku da Wike suna kara magana bayan Atiku ya sanar da Ifeanyi Okowa matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai zuwa.
2. Dabi’ar Wike
Jaridar ta na zargin halayar Gwamnan na Ribas da irin dabi’arsa ta jawo Atiku Abubakar wanda ba mutum ba ne mai hayaniya, ya ki zaben shi a matsayin abokin takara.
Shi Wike mutum ne mai hayaniya da fadan duk abin da ya zo masa ba tare da jin wani tsoro ba. A gefe guda kuwa, Ifeanyi Okowa ya na yanayi da ‘dan takaran na PDP.
3. Kokari a zaben fitar da gwani
Legit.ng Hausa ta na zaton Sanata Okowa ya taka rawar gani wajen nasarar da Atiku Abubakar ya samu a zaben fitar da gwani, inda ya doke Nyesom Wike da wasunsa.
Sakayyar da Atiku zai yi wa Okowa shi ne ya dauke shi a matsayin mataimaki. Daukar Wike zai zama Okowa ya yi biyu babu a 2023 bayan ya yi fada da makwabacin na sa.
4. Atiku v Wike
Tun can dai babu jituwa sosai tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Wike. Rahoton ya ce a zaben fitar da gwani na 2019, Wike ya goyi bayan Aminu Tambuwal a kan Atiku.
Nyesom Wike bai kallon Atiku a matsayin abokin tafiya, sai ma wanda ya baro APC zuwa jam’iyyar PDP domin ya yi takara da shi bayan sun gama wahala da jam’iyya.
5. Kalaman Nyesom Wike
Wasu maganganun Wike za su iya zama matsala a gare shi. Da bakinsa ya taba nuna kiyayyarsa ga Atiku, kuma ya taba cewa bai sh’awar kujerar mataimakin shugaban kasa.
Haka zalika za a iya amfani da wasu babatun Gwamnan na jihar Ribas a yankin Arewacin Najeriya domin a kawowa takarar Atiku da PDP barazana a zaben mai zuwa.