Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace wani Basarake da dansa a jihar arewa


An sace Hakimin kauyen Zira Yahaya Saleh da dansa Habibu Saleh a karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili, ya tabbatar da sace basaraken.

Wakili ya ce ‘yan bindigar sun kai hari kauyen Zira da ke kan iyaka da jihar Filato a daren ranar Asabar din da ta gabata inda suka aikata hakan.

An kuma bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Umar Sanda ya aike da tawagar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa yankin yayin da aka umarci jami’in ‘yan sandan shiyya (DPO) da ya fara bincike da ceto wadanda aka sace.

Rundunar ta kuma yi kira ga mazauna garin da su baiwa ‘yan sanda bayanai masu amfani tare da rokon jama’a da su kwantar da hankalinsu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN