Wata ‘yar Najeriya ta mutu a wani hatsarin mota kwanaki 5 da aurenta


Wata budurwa mai suna Maryam Olawunmi Afolabi Ahmed ta rasu a wani hatsarin da ya faru kwanaki biyar bayan aurenta a jihar Kaduna. 

Maryam wadda dalibar shekarar karshe a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna ta kasance cikin fasinjoji 18 da ke cikin motar bas 18 da suka mutu a wani mummunan hatsarin da ya afku a safiyar ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni a Gidan Kwano, kan hanyar Minna-Bida a cikin karamar hukumar Bosso a jihar Neja.

Wasu mutanen da ke cikin motar bas din da aka ce ta taso ne daga Legas, sun kone kurmus, bayan da direban ya ci karo da wata babbar motar titin da ta lalace a kan hanya.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya bayyana cewa a yanzu haka wani wanda ya tsira da ransa yana kwance a asibitin Minna. 

An yi jana’izar gawarwakin wadanda suka motu a Makabartar Gidan Mangoro da ke wajen Minna, babban birnin jihar. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN