2023: Da yuwuwar za'a ayyana gwamnan PDP mai ci a matsayin mataimakin Atiku


Yayin da jam'iyyun siyasa ke kokarin cike gurbin mataimakan yan takararsu na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ɗan takarar PDP. Alhaji Atiku Abubakar, na gab da tsaida matsaya.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Punch cewa magoya bayan ɗan takaran na ƙunsa gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin mataimakin Atiku.

Matuƙar ba'a samu wani canji a lokacin karshe ba, Me yuwuwa Okowa za'a bayyana a matsayin mataimakin ɗan takara na sahun gaba a tseren ɗarewa kujera lamba ɗaya a 2023

Gwamna Okowa ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Atiku Abubakar a babban taron PDP na zaɓen ɗan takarar shugaban kasa wanda ya gabata a watan Mayu.

Hakan ya ba gwamnan damar gabatarwa da fahimta cikin sauki ga Atiku, ban da wasu taimako da sadaukarwa da gwamanan ya yi wa É—an takaran.

Wata majiya ta ce:

"Okowa ne ya haɗa kan kayan aikin da muka yi amfani da su a zaɓen fidda gwani, shi ne zaɓin da muka fi so duk da wasu na ganin a duba bai wa gwamna Wike da Udom."

A yanzun, bayanan da suka fito daga kwamitin jam'iyyar PDP, da ya ƙunshi gwamnoni, mambobin kwamitin ayyuka NWC, mambobin kwamitin amintattu BoT, ya nuna cewa a yau Talata za'a kawo ƙarshen wanda zai zama mataimaki.

Yayin da Jam'iyyar PDP ke martani kan lamarin ta bakin kakakinta, Debo Ologbunagba, ba ta bayyana ainihin lokaci ba amma ta nuna cewa lokaci zai yi alƙalanci bayan kammala shawara a makon nan.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN