Da dumi-dumi: Fiye da Yan bindiga 200 sun farmaki Masarautar Zuru, sun kone gidaje a garuruwa 7 sun kashe mutane da dama tare da kora fiye da shanaye 2000


Yan bindiga kimanin 200 sun Kai sabon farmaki a kauyukan karamar hukumar Danko Wasagu da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi. Ana zargin sun kashe akalla mutum 11, tare da Kona gidaje da dama daga bisani suka kora shanaye akalla fiye da 2000.

Kafar labarai ta yanar gizo na isyaku.com ya samo cewa maharan sun farmaki kauyukan ne da sanyin safiyar Talata 14 ga watan Yuni 2022.

Ana zargin garuruwa da kauyukan da Yan bindigan suka kai wa farmaki sun hada da Makera, Tungan Taro, Tungan Dan yaki, Sami Boka, Sakdaga, Runtuwa, Donka, Mantare, Yar Danko, Makarantar Nadabo, Kzambu, Kwanan Dutsi, Rijiyar Baure, da Tungan Dorowa.

Maharan sun kone gidaje da dama tare da kora shanaye da ake zargin sun haura 2000.

Yayin da wata majiya ta bangaren mahukunta ta ambaci mutum 11 ne aka kashe, sai dai wani mazauni wannan yankin da baya son mu ambaci  sunansa ya yi zargin cewa tsakanin garin Tungan taro da Tungan Dorowa an sami gawaki 15. Kuma tsakanin garin Sakzaga da D'koliko an sami gawa 15 bayan wadanda ke asibiti.

Alhaji Ibrahim Ganda da jikanshi ne mutanen farko da maharan suka fara kashewa a Tungan taro kafin suka bi sauran jama'a suka yi masu kisar gilla, tare da kwace masu shanaye.

Mun samo cewa soji sun kashe Yan bindiga 5 a yankin Tadurga. Yayin da Yan banga suka kashe Yan bindiga 3 tsakanin Maga da Kyabu.

Sai dai duk da yake jirgin saman yaki na sojin sama ya isa yankin cikin gaggawa, amma jirgin bai saki bama bamai ba domin Yan bindigan sun gudu suka shige cikin garuruwa da kauyukan yankin suka boye.  Majiyar mu ta ce wannan ne dalili da ya sa jirgin bai saki bam ba domin gujewa jefa ban kan bayin Allah mutanen gari. 

Kazalika mun samo cewa soji sun raba kansu gida uku inda suka fuskanci Yan bindigan tare da Jan daga a wasu wurare musamman wajen kare makarantar grin Maga.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN