Za a jefe mutane 51 da duwatsu har su mutu a kasar Iran (Hotuna)

 


Kasar Iran ta yanke wa mutane 51 hukuncin kisa ta hanyar jifa da duwatsu har sai sun mutu bayan an kama su da laifin aikata Zina yayin da suke da aure.

Jimillan mata 23 ne da maza 28 hukuncin ya shafa. Wannan na zuwa ne bayan Alkalai da mahukunta suka ci gaba da sa kafar wando daya da ma'aurata da ke zinace-zinace.

Rahotanni na cewa wadanda lamarin ya shafa suna cikin shekarunsu ne na 20.

A kasar Iran, akan sa wadanda aka yanke wa irin wannan hukunci ne cikin buhu sai a gina rami a saka su har iya kwankwaso kafin a fara jifansu da duwatsu har su mutu. Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN