Wata mahaifiya da ta samu cikin uku ta bayyana yadda ta samu juna biyu tun tana da ciki.
Cara Winhold, mai shekaru 30, da mijinta Blake, mai shekaru 33, sun yi fatan fadada danginsu bayan haihuwar dansu Wyatt a shekarar 2018.
Ma'auratan, daga Texas, na Amurka, sun sami barin ciki har sau uku tare da daya daga cikinsu ya yi kusan mutuwa.
Sannan Cara ta sami ciki a cikin Maris 2021.
A lokacin duban Cara ta gano cewa a zahiri tana tsammanin jarirai biyu da aka samu cikin mako guda.
Babban abin mamaki wanda ba kasafai ake samunsa ba ana Kiran matsalar da superfetation. Wani yanayi ne da mace ke iya daukan cikin duk da cewa tana dauke da ciki tun farko. Yana faruwa a farkon ciki kuma yana iya faruwa kwanaki ko makonni bayan na farko.
Cara ta haifi Colson bayan karfe 4 na safe a ranar 25 ga Oktoba, 2021, tare da Cayden bayan mintuna shida.
Cara ta ce: "Na sami ciki yayin da nake da juna biyu. Na ce wa likita, 'Me ya faru? Ba shi ne karo na farko ba. Me ke faruwa?'
“Ta ce mai yiwuwa na yi kwayaye sau biyu, na saki Æ™wai biyu kuma sun samu takin lokaci daban-daban, kusan mako guda tsakani.
"Ina so in yi imani cewa hanyata ce ta dawo da jariran biyu da na rasa kuma na taimaka musu ta wata hanya.
Rubuta ra ayin ka